Kasar Nijar za ta karbi bakuncin taron shugabannin kasashen mambobi na Conseil de l'Entente wato kwamitin jituwar kasashe biyar na Afrika a ranar 17 ga watan Disamba mai zuwa, a wani labarin da ya fito daga hukumomin Niamey. A gabanin wannan dandali, ministocin harkokin wajen wannan gamayya sun gudanar da wani zaman taron musamman a birnin na Niamey a karshen makon da ya gabata.
Zaman taron da ya taimaka wa wakilan wadannan kasashe biyar mambobin wannan kwamiti dudduba da amince da rahoton da ya shafi kudaden da za'a zuba wajen gudanar da ayyuka da shirye-shiryen da ke cikin jadawalin kwamitin a shekarar 2013, rahoton tafiyar da ayyukan shekarar 2012 da kuma shirin gina layin dogo da zai hade da manyan birare na kasashen mambobin wannan kungiya. (Maman Ada)