A wani ci gaban kuma ma'aikatar sufurin jiragen saman tarayyar Najeriya, ta ce, hare-haren da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kaddamar a Borno, ba su shafi filin tashi da saukar jiragen saman jihar ba.
Kakakin ma'aikatar Yakubu Datti ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua hakan, yana mai cewa, babu bukatar masu amfani da wannan filin jirgi su razana, kasancewar jami'an tsaro na daukar matakan da suka wajaba na dawo da yanayin tsaro.
A bangare guda kuma, wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar Chris Olukolade ya fitar a Abuja, babban birnin kasar, ta ce, sojoji sun hallaka 'yan kungiyar ta Boko Haram su 24, yayin dauki ba dadin da bangarorin biyu suka yi da junan su da sanyin safiyar Litinin. (Saminu)