Wasu mutane da ba tantance da yawansu ba sun rasu, sakamakon wani hari da ake zaton 'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram suka kaddamar da shi, kan sansanin sojin sama dake birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Hukumar 'yan sandan kasar wadda ta tabbatar da faruwar wannan lamari, ta kuma kara da cewa, maharan sun yi wa barikin sojin mai kunshe da bataliya ta 33 tsinke ne, da sanyin safiyar ranar Litinin 2 ga watan nan, suka kuma bude wuta ga jami'an dake ciki. An ce, maharan sun kuma kaddamar da wasu hare-haren na daban, a wata kasuwa dake kan titin Maiduguri zuwa Kano.
Sakamakon aukuwar wannan lamari, mahukuntan jihar sun sanya dokar hana zirga-zirgar jama'a ta sa'o'i 24. Har ila yau, an bukaci al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu, kasancewar jami'an tsaro na daukar dukkanin matakan dawo da doka da oda.
Shi ma kakakin rundunar sojin ta Najeriya dake jihar ta Borno Kanar Muhammad Dole, yayin zantawarsa da 'yan jarida, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ko da yake ya ce, rundunar sojin ta samu nasarar murkushe harin. (Saminu)