in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kashi 70 bisa dari na tsoffin 'yan tawaye a Cote d'Ivoire sun samu guraben aiki yi
2013-12-09 10:28:48 cri

Babban darektan hukumar kula da karbe makamai da janye sojoji da kuma samar da aiki yi ta kasar Cote d'Ivoire (ADDR) Fidel Sarassoro ya bayyana a ranar Lahadi a birnin Abidjan cewa, tsarin shigar da tsoffin mayaka bayan rikicin siyasa a cikin harkokin tattalin arziki da na jama'a na samun cigaba.

A cewar mista Sarassoso a yayin wata hira tare da manema labarai, kashi 70 bisa dari na tsoffin 'yan tawaye, an shigar da su ne a cikin ayyukan jama'a bisa ga dubu 30 da aka tsai da a wannan shekarar 2013.

Burinmu a wannan shekarar 2013 shi ne shigar da tsoffin mayaka dubu 30, a yanzu mun kammala kashi 70 cikin dari na adadin wannan buri da muke son cimma, in ji mista Sarassoso.

A cewarsa, adadi ne da ya dace, ganin cewa, gwamnatin kasar Cote d'Ivoire da abokan hadin gwiwarta na cigaba da kokarinsu bisa manufar shigar da tsoffin mayakan kasar, ta yadda za su samu aikin yi yadda ya kamata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China