Ministocin ma'aikatun albarkatun ruwa da noman rani na kasashen Sudan da Masar da Habasha za su gudanar da karin shawarwari, don gane da batun ginin wata katafariyar madatsar ruwa a Habasha, wadda za ta rika samun ruwa daga kogin Nilu da ya ratsa yankunan kasashen uku.
Wakilan kasashen uku ne dai suka yanke shawarar kiran taron na gaba a ranar Litinin 4 ga wata. Da yake karanta takardar bayan taron, ministan ma'aikatar albarkatun ruwa da wutar lantarki na kasar Sudan Osama Abdallah, ya ce, taron na ranar Litinin ya ba su damar gayawa juna hakikanin gaskiyar halin da ake ciki, sun kuma yanke shawarar sake gudanar da wani zaman tattaunawar a birnin Khartoum na kasar Sudan, ranar 8 ga watan Disambar dake tafe.
Abdallah ya ce, makasudin shirya ganawar shi ne, kokarin cimma matsaya guda don gane da wannan bukata, ta ginin babbar madatsar ruwa a Habasha, matakin da ka iya shafar bukatun daukacin kasashen uku. (Saminu)