in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne shirin mayar da 'yan gudun hijirar Somaliya ya zama bisa yardarsu, in ji UNHCR
2013-11-27 10:45:32 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana cewa, wajibi ne shirin da ake yi na mayar da 'yan gudun hijirar kasar Somaliya kimanmin 500,000 da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar Dadaab da ke arewacin kasar Kenya zuwa kasarsu, ya kasance bisa amincewarsu.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta bayar ranar Talata a Nairobi, babban binrin kasar kenya, tana mai cewa, da farko za a fara aiwatar da shirin ne ta hanyar mayar da hankali wajen taimakawa shiri na gwaji, inda a halin yanzu aka fara tattaunawa da wasu yankuna guda 3 da ke Somaliya don gudanar da wannan shiri, wadanda suka hada da Luuq, Baidoa da Kismayo, inda shirye-shirye suka yi nisa tsakanin kasashen Kenya da Somaliya don fara aiwatar da shirin na gwaji.

Wannan sanarwa da hukumar da UNHCR ta bayar, ta zo ne bayan wani umarni na ba zata da sakataren kula da harkokin cikin gida na kasar Kenya, Joseph Ole Lenku ya bayar na rufe sansannin, bayan ziyarar da ya kai sansanin na Dadaab a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce, gwamnati ba za ta canja ra'ayinta game da shirin mayar da 'yan gudun hijirar ba, kana ya bukaci kungiyoyin agaji da ke aiki a sansanin, da su mayar da ayyukansu zuwa yankunan masu tsaro a Somaliya.

Lenku ya kuma shaidawa 'yan gudun hijirar cewa, za a fara shirin ne kamar yadda aka tsara a watan Janairun shekara ta 2014, inda ya ce, ba gudu ba ja da baya a shirin, kuma lokaci ya yi da za a yi adabo tare da yiwa 'yan gudun hijirar fatan alheri yayin da suka koma gidajensu, inda ake fatan za su taimaka wajen sake gina kasarsu.

Amma, hukumar UNHCR ta ce, sakamakon yarjejeniyar da aka sanya hannu a kai a ranar 10 ga watan Nuwamba game da shirin mayar da 'yan gudun hijirar tsakanin hukumar ta UNHCR, gwamnatocin Kenya da Somaliya, hukumar ta UNHCR da Kenya sun nanata cewa, kamata ya yi batun mayar da 'yan gudun hijirar ta Somaliya zuwa kasar tasu, ya kasance bisa radin kansu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China