A ranar Laraban nan 23 ga wata, rundunar sojojin Nigeriya ta 7 a garin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar ta tabbatar da kame wadansu mutane 6, jim kadan da saukar su a filin jiragen sama bayan dawowa daga kammala aikin haji a kasar Saudiya wadanda ake zargin cewa, su jiga jigan mambobin kungiyar nan ne ta Boko Haram.
Aliyu Danja, kakakin rundunar sojin wanda ya sanar da kamen ga manema labarai a Maiduguri ya ce, wadanda aka kama ana zargin cewa, suna da karfi a cikin kungiyar, kuma an yi nasarar kama su ne a ranar Litinin bayan saukar jiragen dake dauke da alhazai domin a yi musu tambayoyi.
Sai dai ya yi bayanin cewa, uku daga cikin mutane 6 da aka kama, an riga an sallame su sakamakon tabbatar da cewar, ba su da wani alaka da kungiyar, amma sauran uku na nan tsare.
Haka kuma kakakin ya ce, rundunar ta kaddamar da wani sabon salon na zagaya gari domin ba da tsaro mai karfi a kan manyan hanyoyi domin a shawo kan harin da 'yan kungiyar ke kai wa matafiya. (Fatimah)