Wata kotu a kasar Masar a ranar Litinin din nan 21 ga wata ta yanke shawarar dage sauraran shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak zuwa 16 ga watan gobe na Nuwamba bayan kwanaki uku da aka yi ana sauraran shaidu daga tsaffin jami'an tsaron kasar a sakaye, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya bayyana.
Hosni Mubarak, 'dan shekaru 85 da haihuwa, an yanke masa hukuncin rai da rai ne a gidan yari a bara game da zargin hada baki wajen tunzura tashin hankali da kisan masu zanga-zanga lokacin boren da jama'ar kasar suka yi mashi a shekarar ta 2011, sai dai wata kotun daukaka kara ta ba da umurnin a sake duba shari'ar.
An dai saki Mubarak daga gidan yari a watan Agustan wannan shekarar, amma za'a cigaba da tsare shi a wani daki cikin asibitin sojoji na Maadi dake kudancin Alkahira, babban birnin kasar. (Fatimah)