in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mayaka sun hallaka matasa 14 a arewacin Najeriya
2013-08-27 09:49:00 cri

Mahukunta a Najeriya sun tabbatar da kisan wasu matasa dake taimakawa jami'an tsaro su 14 a garin Bama dake jihar Borno a tarayyar Najeriya.

Wani jami'in hukumar garin na Bama Shehu Gulumba dake tabbatar da faruwar wannan lamari, ya ce, samarin sun rasa rayukansu ne ranar Lahadi 25 ga wata, bayan da wasu mahara da suka yi shigar jami'an tsaro suka yi musu tayin zuwa wani taron tattaunawa, daga bisani kuma suka yi musu kwantan bauna a hanyarsu ta halartar taron.

Wadannan dai matasa masu gudanar da ayyukan tsaro na sa kai, na cikin gungun samari ne dake taimakawa jami'an tsaron kasar wajen kame magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram, kungiyar da ta shahara matuka wajen kaddamar da hare-hare a sassan arewacin kasar tun daga shekarar 2009.

Aukuwar wannan balahira dai na zuwa ne mako guda da shelanta kashe madugun kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau, da rundunar sojin kasar ta ce ta yi, yayin wani dauki ba dadi da ya auku tsakaninta da maharan kungiyar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China