in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin da Habasha sun kulla yarjejeniyar aikin shimfida hanyar jiragen kasa
2011-10-26 15:18:00 cri
A ranar 25 ga watan Oktoba kanmafanin dillanci labarai na Xinhua ya rawaito cewa, hukumar jiragen kasa ta kasar Habasha da kamfanin jiragen kasa na kasar Sin (CERC) a ranar Talatar da ta gabata sun kulla yarjejeniyar aiki ta gina hanyar jirgin kasa wadda zata fara daga cikin garin Sebeta wanda yake da nisan kilomita 25 daga Adis Ababa zuwa Meiso dake gabas da birnin.

A cewar hukumar kamfanin jiragen kasa ta Habasha ,tsawon layin dogo da za a shimfida zai kai kilomita 320.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin kulla yarjejeniyar wanda aka yi a ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha, sun hadar da ministan harkokin wajen kasar Hailemariam Desalangne ,da karamin ministan sufuri na kasar Getachew Mengiste,da shuagaban hukumar kula da hanyoyin Adis Ababa Fekadu Haile, sai jakadan kasar Sin a Habasha Gu Xiaojie, da Qian Zhaogang, jami'in tuntuba harkar kasuwanci dake ofishin jakadacin kasar Sin a Habasha.

Hailemariam wanda shi ma ya kasance mataimakin firamintan kasar ta Habasha, ya yaba da kwarrarun kamfanin na CERC,wadanda suka sheda kwarewa wajen tsara layin dogon da za a shimfida.

Daga karshe jakadan Sin Mr Gu,yayi alkawarin baiwa kamafanin na CERC cikkaken goyon baya lokacin da zai gudanar da aikin a kasar ta Habasha.(Salamatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China