in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Madagascar ta ce, komi ya kammala game da shirya zaben shugaban kasa
2013-10-21 10:47:52 cri

Shugabar hukumar zabe mai zaman kanta ta wucin gadi (CENIT) a kasar Madagascar, madam Atallah Beatrice ta bayyana a yayin wani taron manema labaru a kwanan baya cewa, dukkan ayyukan shirye-shiryen zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Oktoba da muke ciki sun kammala baki daya.

Katunan zabe da za'a rabawa masu zabe miliyan bakwai da dubu dari takwas da ishirin da biyar da dari uku da biyar, an riga an buga su tun bayan da aka fitar da rajistan sunayen masu zabe na karshe a ranar 9 ga watan Oktoban, wadanda tuni aka fara rarraba su tun ranar 10 ga watan Oktoba, in ji wannan jami'a.

Game da batun kayayyakin zabe, musammun ma kuri'un zabe, rumfunan zabe da kuma akwatunan zabe sun riga sun isa a yankuna 119, kana za'a isar da su zuwa cibiyoyin zabe 20001 a ranar 23 ga watan Oktoba mai zuwa in ji madam Atellah Beatrice. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China