in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da wani yunkurin kasa da kasa domin kare 'yan kaka gida
2013-10-13 17:18:34 cri
Ya kamata gamayyar kasa da kasa ta dauki matakan kare 'yancin 'yan kaka gida da kuma rigakafi bala'in nutsewar jiragen ruwa dake jigilar bakin haure a teku, in ji babban magatakarda na MDD mista Ban Ki-moon.

Mista Ban ya yi wannan sanarwa bayan ya samu rahoton dake bayyana mutuwar wasu bakin haure bayan jirgin dake dauke da su ya nutse a gabar kasar Italiya, kwanaki kadan bayan babban hadari ya abku kusa da tsibirin Lampedusa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 300..

Sakataren janar na MDD na kira ga gamayyar kasa da kasa da ta dauki matakai domin ganin cewa, irin wadannan hadarurruka ba za su sake abkuwa ba a nan gaba, har ma da matakan da suka shafi dalilan dake janyo wannan bala'i, ta yadda za a kare 'yan kaka gida. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China