in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Larabawa da na Afrika na kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashensu
2013-11-20 14:24:27 cri

Fiye da masu fada a ji ko wakilai 71 daga kasashen Larabawa da na Afrika suka hadu a ranar Talata a kasar Kuwaiti a karo na uku na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa domin kokarin cimma wata sabuwar dangantakar hadin gwiwar cin moriyar juna.

Zaman taron na kwanaki biyu, mai jigon "Abokan hadin gwiwa kan cigaba da zuba jari" na gurin kafa wata sabuwar dangantaka ta tushe da za ta taimakawa kasashen yankunan biyu da ke fuskantar manyan kalubaloli.

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba a nasa bangare ya bayyana cewa, ya kamata a samu hadin gwiwa da hada kai daga dukkan fannoni domin fuskantar kalubalolin da kasashen Afrika suke fama da su, kamar tashe-tashen hankali da ta'adancin kan iyakoki domin cimma maradun cigaba mai karko da zaman lafiya.

Haka kuma ya jaddada muhimmancin kafa sahihiyar dangantaka tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa, ta yadda za'a iyar samun karin zuba jarin kasashen Larabawa a nahiyar Afrika a fannonin cigaban zaman rayuwar jama'a da kiyaye muhalli.

Sarkin Kuwaiti, Cheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-sabah da ya jagorancin bikin bude dandalin ya bayyana cewa, taron na jaddada niyyar kasashe mahalarta taron wajen bunkasa dangantakar hadin gwiwa domin fuskantar kalubalolin da kowa ya sani tare da tsallake shingayen dake hana mu cimma muradin cigaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China