Kwamitin tsaro na MDD ya amince da karfafa aikin tawagar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM), zuwa wani 'dan lokaci a ranar Talata domin tabbatar da tsaro a wannan kasa da kuma fuskantar bazaranar mayakan kungiyar Al-Shabaab.
Ta hanyar tsai da wani kuduri bisa rinjaye na mambobi goma sha biyar, kwamitin ya kara tsawon wannan wa'adi na aikin AMISOM har zuwa ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2014, tare da bukatar tarayyar kasashen Afrika da ta kara yawan sojojinta daga 17731 zuwa 22126, sannan kuma MDD za ta kara samar da kayayyakin aiki.
Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa, matakin kara yawan sojojin zai kara karfin sojojin AMISOM cikin gajeren lokaci.
Sakatare janar na MDD da tarayyar Afrika sun sake bukaci a kara kwarin gwiwar wannan tawaga, musammum ma wajen amfani da jirage masu saukar ungulu, ta yadda za a yaki da dakarun Al-Shabaab. A cikin wannan kuduri, kwamitin tsaro na MDD ya kuma dauki niyyar bisa ra'ayin mista Ban Ki-moon na tura tawagar sojojin MDD domin kiyaye tsaron cibiyoyinta dake wannan kasa. (Maman Ada)