A ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Qin Gang, kasar a ko da yaushe ta yi imanin cewa, tattaunawa da hadin gwiwa su ne hanyoyin da za a bi a fuskanci wannan matsalar ta makamashin nukiliyar kasar Iran din.
A karkashin yarjejeniyar da aka sanya ma hannu a Tehran, kasar ta Iran za ta amince da jami'an hukumar ta IAEA su ziyarci sansanin sarrafa nukiliya ta Arak da kuma mahakan ma'adinai na Gachin. Abin da a cewar Mr. Qin, wata dama ce mai muhimmanci ta tattaunawa game da batun nukiliyar, don haka Sin na maraba sosai da wannan hadin kai tsakanin bangarorin biyu.
A cewar shi, kasar Sin ta yarda cewa, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen bullo da dabarun warware matsalar nukiliya ta Iran din mai sahihanci kuma yadda ya kamata.(Fatimah)