in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashoshin shan mai za su iyar daina aiki dalilin yajin aiki daga Litinin a Afrika ta Kudu
2013-09-09 15:52:08 cri

Direbobin motocin kasar Afrika ta Kudu sun garzaya zuwa tashoshin shan mai a ranar jiya Lahadi bisa tsoron yajin aikin gama gari na ranar yau Litinin. Ma'aikata kusan dubu 72 za su kaucewa aiki bayan da aka kasa cimma bakin zare domin warware sabani kan batun karin albashi tsakanin kungiyar ma'aikatan karfe ta kasar Afrika ta Kudu (NUMSA) daga bangare guda da kungiyar masu sarin mai (FRA) da kuma kungiyar masana'antun kera motoci (RMIO), yajin aikin da aka tsai da gudanarwa a makon da ya gabata, an gusa shi domin ba wai ma'aikata damar yin nazari kan bukatun kungiyar NUMSA na neman karin albashi na Rands talatin kwatankwacin dalar Amurka uku duk awa daya, wannan kuma ga dukkan ma'aikatan dake samun fiye da Rands dubu shida a ko wane wata daga bakin shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China