MDD ta baiyana ranar Laraba cewa, za ta samar da karin kudaden tallafi ga al'ummomi dake cikin kunci a kasar Sudan ta Kudu da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 33.
Mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey ya bayyana cewa, kudaden daga asusun tallafawa bil adama na kasar Sudan ta Kudu zai taimaki kungiyoyin ba da agaji wajen isa ga jama'a dake matukar bukatar taimako a fuskar ruwan sha, tsabta, ilmi, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, tallafawa rayuwa da kawar da nakiya da aka dasa.
Ya ce, mutane sama da miliyan 4 ne ba su da isashen abinci a Sudan ta Kudu, kana sama da dubu 70 ba su da matsuguni tun farkon shekarar nan.
Kididdiga na MDD ya nuna cewa, sabuwar kasar na da 'yan gudun hijira dubu 220, mafi yawansu daga kasar Sudan. Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan ne ran 11 ga watan Yulin shekarar 2011.
Ci gaban fadace fadace tsakanin kabilu a jihar Jonglei ta kasar Sudan ta Kudu ya yi sanadin barnatar da rayuka, kana dubban jama'a na kaura daga gidajensu.
A makon da ya gabata, asusun ba da agajin gaggawa na MDD ya amince da bayar da dalar Amurka miliyan 6 ga kungiyoyin agaji don su samar da abinci, kayan gina jiki, ruwan sha mai tsabta ga al'umommi da abin ya shafa a Jonglei.
Asusun zai taimaka a ciyar da mutane dubu 60 cikin watanni masu zuwa. (Lami)