in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi hasashen ganin kusufin rana a Nigeria
2013-10-30 09:48:03 cri

A Najeriya, hukumar binciken sararin samaniyar kasar NASRDA, ta sanar da hasashen faruwar kwarya-kwaryar kusufin rana a ranar Lahadi mai zuwa.

Da yake tabbatar da hakan, babban daraktan hukumar ta NASRDA Seidu Mohammed, ya ce, kusfewar ranar za ta shafi sassan kasar da dama, don haka ya shawarci al'ummar kasar da su kwantar da hankalinsu, kasancewar kusfewar ranar ba za ta haifar da wata matsala gare su ba.

Ya ce, ga masu sha'awar kallon ranar yayin da take lullube, akwai bukatar su sanya tabarau na kariya domin kaucewa illa ta idanunsu.

A cewar Mohammed, baya ga Najeriya da dama daga kasashen dake nahiyar Afirka za su ga wannan kwarya-kwaryar kusufi, yayin da kuma wasu kasashen duniya za su gamu da cikakken kusufin na ranar.

Har ila yau, babban daraktan hukumar ta NASRDA ya ce, 'yan Najeriya za su ga wannan kusufi na rana a nan gaba cikin watan Afirilun badi, da watan Maris na shekarar 2015, da kuma watan Satumbar shekarar 2016. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China