Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a ranar Laraban nan 23 ga wata ta yi tir da abin da ta kira kokarin tada zaune tsaye a kasar Mozambique, ta hanyar kawo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, har ma da cigaban kasar baki daya.
A cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta fitar, ta ce, kungiyar tana sa ido sosai a kan yanayin da ake ciki a kasar ta Mozambique yanzu haka.
Shugabar ta nuna damuwar ta musamman a kan sanarwa da kungiyar adawa da gwamnati Renamo ta yi na cewa, ta janye daga yarjejeniyar sulhu da ta rattaba wa hannu tare da gwamnatin kasar a shekara ta 1992.
Ta jaddada rashin amincewar AU a cikin duk wani kokarin da zai kawo rashin zaman lafiya da daidaito a kasar, musamman ma abin da zai shafi cigaban tattalin arzikin da aka samu ya zuwa yanzu.
Madam Nkosazana Zuma ta nuna muhimmancin dake akwai ga daukacin wadanda ke da ruwa da tsaki da su yi iyakacin kokarinsu na tattaunawa tare da kai zuciya nesa domin ba da dama ga kasar da ta samu cigaba a kan hanyarta ta bunkasuwa, ta kuma kara tantance hanyoyin aiwatar da demokuradiya da suka hada da nasarar gudanar da babban zaben da ake shirin yi a watan Nuwamban nan mai zuwa. (Fatimah)