in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mozambique ya ce, abin da sojojin kasar suka yi a kare kai ne
2013-10-23 10:11:25 cri

Shugaban kasar Mozambique Armando Guebuza a ranar Talatan nan ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun mai da martani ne domin kare kansu lokacin samamen da suka kai wa kungiyar 'yan adawa Renamo, kamar yadda kafar watsa labaran kasar ta sanar.

Wannan furuci na shugaban kasar ya biyo bayan samamen da sojoji suka kai maboyar shugaban kungiyar 'yan adawa dake cikin daji a wani wuri mai duwatsu na yankin Satungira bayan da suka kewaye shi na tsawon kwanaki biyu, abin da ya sa shugaban kungiyar Alfonso Dhlakama tserewa, ya bar gidan nashi inda yake zaune a ciki fiye da shekara daya.

Game da hakan, kakakin kungiyar ta Renamo Fernando Mazanga a cikin wata sanarwa a yammacin ranar Litinin din ya ce, harin da sojojin suka kai ya nuna alamar dakatar da yarjejeniyar sulhu ta tsawon shekaru 21 da kungiyar ta cimma tsakaninta da gwamnati a birnin Rome wadda ta kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru 16 da aka yi, abin da kuma yanzu ya kawo fargaba ga al'ummar kasar game da tsaro da kwanciyar hankali a nan gaba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China