Mahaukaciyar guguwa da ta ratsa yankunan gabar Puntland dake arewa maso gabashin kasar Somaliya ta kashe mutane 300, in ji hukumomin yankin Puntland.
Ruwa da iska masu karfin gaske tare da ambaliyar ruwa sun janyo matsalar ba zata, mutane 300 ake zaton sun mutu, kuma wasu daruruwa sun bace, sannan an samu asarar dabbobi masu tarin yawa, in ji shugabannin wannan yankin.
Yankin na Puntland ya ci karo da guguwar a ranar Asabar da ta gabata inda aka samu ruwa kamar da bakin kwarya da suka janyo ambaliya da ta lalata manyan hanyoyin sufuri dake shiga wuraren dake fama da wannan bala'i.
Jami'an gwamnatin Somaliya da hukumomin wuraren suna neman taimakon gaggawa zuwa wadannan wuraren dake gabar bakin ruwa a arewa maso gabashin kasar.
Hanyoyin da guguwar ta lalata na kasancewa wata babbar matsala dake kawo cikas wajen kai taimako ga wadannan wurare, in ji hukumomin Somaliya.
Tuni dai hukumomin kasar sun tura jami'an tsaro domin kawo taimako ga wadannan wuraren da guguwar ta shafa.
Haka kuma shugabannin yankin Puntland sun kai ziyara a wuraren da bala'in ya shafa domin kimanta barnar da guguwar ta janyo da kuma sake yin kira ga gamayyar kasa da kasa domin taimaka wa mutanen da suka tsira daga wannan bala'i mafi muni da kasar Somaliya ta gamu da shi. (Maman Ada)