A ranar Laraba 30 ga watan Oktoba ne, mataimakin babban sakataren MDD Jan Eliasson, ya yi kira ga kwamitin sulhun na MDD, da ya mara baya ga kokarin da dakarun da ke aikin wanzar da tsaro a kasar Somaliya.
Eliasson ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yiwa kwamitin tsaron mai wakilai 15 bayani bayan dawowarsa daga Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya, inda ya ce, muddin babu ingantattun matakan tsaro, duk wani kokari da gwamnati da al'ummar Somaliya da kuma sassan da abin ya shafa ke yi zai zama aikin banza.
Ya ce, harin da aka kai a watan Yuni kan ofishin MDD a Mogadishu da harin ta'addancin da aka kai kan rukunin shagunan nan da ke Nairobi a watan Satumba, ya nuna niyyar kungiyar masu kishin Islama na Al-Shabaab ta haifar da barazana da zaman kunci ga 'yan kasar ta Somaliya, domin su yi kokarin kawo zagon kasa ga shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.
Don haka, ya ce, wajibi ne a goyi bayan tawagar kungiyar AU da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya (AMISOM) tare da zuba jari kan dakarun Somaliya da kare rayukan ma'aikatan tawagar da ke gudanar da wannan aiki mai muhimmanci. (Ibrahim)