in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ruwa da iska mai karfi sun hallaka mutane akalla 100 a Somaliya
2013-11-12 10:01:09 cri

Rahotanni daga jihar Puntland ta kasar Somaliya, na cewa, akalla mutane 100 ne suka rasu, baya ga wasu daruruwa da kawo yanzu ba a tantance da halin da suke ciki ba, bayan da wata iska mai karfi, hade da ruwa kamar da bakin kwarya, suka aukawa yankunan dake jihar ta Puntland dake arewa maso gabashin gabar ruwan kasar ta Somaliya.

Bayanai da mahukuntan yankin na Puntland suka fitar sun bayyana garuruwan Eyl, da Beyla, da Dangorayo, da Hafun dake yankin Garduush, da kuma gundumar Alula dake arewa maso gabashin gabar ruwan kasar ta Somaliya, a matsayin yankunan da wannan annoba ta aukawa a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata.

Tuni dai aka bayyana wannan yanki a matsayin wurin da annobar ta aukawa, yayin da kuma mahukunta suka bukaci samar da tallafin kasa da kasa, domin tallafawa al'ummun da abin ya shafa.

Har ila yau mahukuntan jihar ta Puntland sun bayyana kafa wani kwamiti, da zai jagoranci lura da aikin ceto, tare da ba da agaji, musamman a fannin samar da tsaftataccen ruwan sha, da abinci, da magunguna da kuma wuraren fakewa na wucin gadi.

Hakazalika raohotanni sun bayyana cewa, an riga an fara kafa wuraren fakewa a kauyukan dake daf da wannan yanki, tare da bukatar al'ummar dake sassan su ba da nasu tallafi ga wadanda annobar ta aukawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China