Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da kisan fararen hula, tare da raunata wasu da dama a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, ciki hadda wani jami'in rundunar wanzar da zaman lafiya na kasar Tanzaniya, sakamakon sake barkewar fadace-fadacen baya bayan nan.
Kwamitin wanda ya nuna takaicinsa don gane da yadda rundunar mayakan kungiyar nan ta 'yan tawayen M23 ke kaiwa fararen hula, da dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya ta MONUSCO hare-hare, ya ce, farmakin baya bayan nan da aka kaddamar a tuddan Kibati dake Arewacin Kivu ya haifar da barna mai yawa. Kuma MONUSCO na ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da rundunar sojin kasar ta Congo, a yunkurin da ake yi na baiwa fararen hula mazauna yankunan dake da yawan jama'a kariya.
Wata sanarwa da kwamitin tsaron ya fitar, wadda kuma ke kunshe da sakon jaje ga mahukuntan kasar ta Tanzaniya, da ma iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon barkewar rikicin, ta kuma yi kira da babbar murya ga mahukuntan jamhuriyar dimokaradiyyar ta Congo, da su gaggauta gudanar da bincike kan aukuwar lamarin, tare da hukunta masu hannu cikin wannan ta'asa.
Kwamitin tsaron mai mambobi 15, ya sake jaddada bukatarsa ga kungiyar M23, da ma ragowar dakaru masu dauke da makamai, da su dakatar da bude wuta, su kuma kauracewa daukar dukkanin wasu matakai na tada zaune tsaye. (Saminu)