Masu shiga tsakani na kasar Isra'ila da Falasdinu sun gana a yamman ranar Litinin a garin Jericho ba tare da manema labarai suka halarta ba, kamar yadda wata majiya mai karfi ta Falasdinu ta tabbatar.
Majiyar da ta yi bayani a asirce ta shaida ma Xinhua cewa, manyan masu shiga tsakanin sun gana ne a gidan babban mai shiga tsakani na Falasdinu Saeb Erekat ba tare da wakilan Amurka wadanda su ne suka dauki nauyin wannan ganawa ba.
A lokacin ganawar, Erekat ya mika korafinsa ga wakilin Isra'ila game da kisan da wutar bindigar sojojin Isra'ila suka yi ma wassu Falasdinawa 3 a arewacin Ramallah, abin da majiyar ta ce, Isra'ila ba ta karyata ba, ba ta kuma amsa laifinta ba.
Ganawar ranar Litinin dai, an yi ta ne duk da sanarwar farko da Yasser Abed Rabbo, wani mai fafutukar 'yancin Falasdinawa na PLO ya yi cewa, Falasdinu ta dakatar da tattaunawar.
A wani labarin kuma, kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ba da rahoton cewa, shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya gana a ranar Litinin din nan da Janar John Alan, manzon musamman na rundunar tsaron Amurka a wannan yankin, a ofishinsa dake Ramallah.
A lokacin ganawar dai, Janar Alan ya mika wasika ga Abbas wanda ke jaddada goyon bayan samar da zaman lafiya da Amurka ke yi a kan matakin samar da 'yancin kai ga yankin Falasdinu.
An dawo da tattaunawar zaman samar da lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila a watan da ya gabata ne bayan dakatar da aka yi kusan shekaru uku dangane da takaddamar da ake na gina sabbin matsugunar Yahudawa da Isra'ila ta yi a gaban kogin yamma da gabashin Jerusalem, yankunan da suka fada cikin sabuwar kasar Falasdinu a nan gaba. (Fatimah)