in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta rage taimakon kudin da ta bai wa Masar
2013-10-10 10:27:21 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka a ranar Laraban nan ta sanar da jinginar da wani kaso daga taimakon kudin da ta saba bayarwa kasar Masar a duk shekara na kimanin kudin dala biliyan 1.5 domin mai da martani ga halin da Masar din take ciki, inda ta dakatar da kai kayayyakin aikin na'ura na soja da kuma tsabar kudi ga gwamnatin.

Kakakin ma'aikatar Jen Psaki wadda ta sanar da hakan ta ce, Amurka za ta ci gaba da rage kasonta na samar da wassu kayayyakin aiki na na'ura ga rundunar soji da tsabar kudi ga gwamnatin Masar din, har sai an samu wani cigaba mai gamsarwa game da yanayin da ake ciki da ya hada da kafa gwamnatin demokradiya karkashin zabe cikin adalci da gaskiya.

Ma'aikatar sai dai ba ta sanar da adadin nawa za ta rage daga kason da ta saba bayarwa ba.

Madam Psaki ta ce, sakamakon nazarin da shugaba Obama ya umarta a yi, Amurkan ta yanke shawarar cigaba da huldar diplomasiya da gwamnatin ta Masar, sai dai za ta rage adadin taimakon da ta saba bayarwa duk shekara domin kare bukatunta. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China