Wani kwararren malamin jami'an, kuma marubuci 'dan asalin kasar Angola mai suna Luis Kandjimbo, ya shiga jerin mambobin kwamitin kungiyar kula da ilimi da kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin duniya, UNESCO.
Bisa gayyatar da aka yi masa, yanzu haka Kandjimbo zai kasance jami'in tsare-tsare, a kwamitin dake kunshe da kwararru 17, da aka dorawa alhalin rubuta tarihin nahiyar Afirka kashi na 9.
An ce dai wannan aiki zai mai da hankali ne ga zakulo matsalolin da harkar ci ranin ma'aikata da kasashen Afirka ke haifarwa, tare da yiwa ragowar rubuce-rubucen da aka yi kan tarihin nahiyar gyare-gyare, musamman wadanda suka yi daidai da sakamakon sabbin bincike da aka yi game da tarihin nahiyar.
A cewar kamfanin dillancin labarum kasar Angola, kafin wannan gayyata da aka yi masa, Kandjimbo, ya kasance daraktan babbar sakatariyar kasashe masu amfani da harshen Portugese. (Saminu)