in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taliban na Afganistan ta tabbatar da bude ofishinta na tuntuba a Qatar
2013-06-19 10:44:53 cri

Kungiyar Taliban na kasar Afganistan a jiya Talata 18 ga wata ta tabbatar da bude ofishinta na tuntuba a birnin Doha na kasar Qatar domin samar da damar tattaunawa da wassu manyan kungiyoyi, in ji sanarwar da kungiyar ta fitar.

Zabiullah Mujahid, wanda yake ikirarin shi ne kakakin kungiyar, a cikin sanarwar ya ce, Taliban za ta yi amfani da ofishin tuntubarta na Doha domin cigaba da hulda da MDD da sauran manyan kungiyoyi na kasashen waje, da ma na cikin gida, sannan kuma za ta yi amfani da wurin domin inganta dangantakarta da kasashen duniya.

Tun da farko dai, a jiya Talata, kafofin yada labarai na kasar Afganistan sun sanar da cewa, Amurka za ta tattauana cikin lumana da kungiyar a Qatar. Idan har kungiyar ta amince za ta tattauana da ita, hakan zai zama karo na farko da za su yi ganawar gaba da gaba tsakanin kasar da kungiyar.

Sai dai Mujahid bai ce ko za su gana da Amurka ba.

Ba tare da ba da wani karin bayani ba, Mujahid ya ce, za'a yi amfani da ofishin domin ganawa da wassu manyan masu fada a ji a Afganistan, haka kuma za'a yi amfani da ofishin domin fitar da duk wassu sanarwar da ya kamata game da yanayin siyasar da ake ciki yanzu a kasar ta Afganistan ga kafofin yada labarai.

Shugaban Afganistan Hamid Karzai dai a jiya Talata ya sanar da cewa, tawagar tattauna samun zaman lafiya da kungiyar Taliban za su isa birnin Doha domin tattaunawa kai tsaye da kungiyar.

Karzai dai da wassu manyan shugabanni sun dade suna ta yin tattaunawa da kungiyar ta Taliban, amma kuma kungiyar ta ki amincewa, tana mai cewa, babu wata tattaunawar da za'a yi, sai an janye sojojin kasashen waje daga cikin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China