Wata kotu a kasar Mali za ta yi bincike kan mutuwar 'yan jaridar kasar Faransa biyu bayan wasu mutane dauke da makamai sun yi awon gaba da su a ranar Asabar a Kidal, in ji kakakin gwamnatin kasar Mali, Mahamane Baby a ranar Lahadi bayan wani zaman taron gaggawa da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya jagoranta kan wannan matsala ta ba zata.
A yayin taron, shugaba Ibrahim Boubarcar Keita, da faraministansa da ministocin da wannan lamari ya shafa sun tattauna kan yanayin sace 'yan jaridar rediyon kasar Faransa RFI, in ji ministan kwadagon kasar Mali kuma kakakin gwamnati, Mahamane Baby.
Haka zalika taron ya mai da hankali kan matsalar tsaro a dukkan fadin kasar tare da bayyana matakan da za'a dauka, har da batun kafa kwamitin shari'a da zai binciki wannan lamari a kasar Mali, in ji mista Baby.
Jami'an ya kuma jaddada cewa, shugaban kasar Mali da gwamnatinsa na gudanar da ikon kasar Mali a dukkan fadin kasar, har ma da Kidal tare da kuma cewa, za'a tabo wannan batu a yayin wata ganawa tare da sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon da zai isa birnin Bamako mako mai zuwa. (Maman Ada)