Babban bankin duniya da kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun alkawarta baiwa yankin Sahel gudummawar kudi, da yawansu ya haura dala miliyan dubu 8, domin bunkasa ci gaba, da fidda dinbin al'ummun yanki daga kangin talauci.
Wannan alkawari na zuwa ne bayan da babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, suka isa Mali domin gudanar da ziyarar aiki.
Da yake tsokaci don gane da halin da ake ciki a wannan yanki na Sahel, Ban Ki-Moon, ya ce, kalubalen dake addabar wannan yanki ya shafi daukacin kasashen duniya, don haka akwai bukatar dukufa tukuru domin magance yaduwarsa.
Rahotanni da MDDr ta fitar sun bayyana cewa, wannan yanki na Sahel ya yi fama da fari har sau uku tsakanin shekaru 10 da suka gabata, yayin da mutane da yawansu ya zarta miliyan 10 ke zaune a wannan yanki cikin hali na rashin isasshen abinci, ciki hadda yara kanana miliyan 5, dake fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Har ila yau, rahoton na MDD ya bayyana rashin ingantaccen tsarin siyasa, da sauyin gwamnatoci ba bisa tsarin da doka ta tanada ba, a matsayin manyan dalilan nakasu, da fannin tattalin arziki da zamantakewar al'ummun yankin na Sahel ke fuskanta.
Wannan yanki na Sahel dai na kunshe da yawan al'ummar da ta kai miliyan 80, daga kasashen Mauritania da Eritrea, da Burkina Faso. Ragowar su ne, kasashen Chadi, da Mali, da Niger, da Nigeria, da Senegal da kuma kasar Sudan. (Saminu)