Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da aka yiwa masu aikin kiyaye zaman lafiya yayin wani sabon fadan da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a yankin gabashin jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC).
Ban Ki-moon ya yi wannan kalaman ne ranar Lahadi 27 ga wata cikin wata sanarwa da kakakinsa ya bayar, yana mai cewa, babban sakataren ya nuna matukar bacin ransa kan yadda 'yan tawayen M23 suka budewa masu aikin kiyaye zaman lafiya 'yan kasar Tanzaniya wuta a gabashin kasar.
A cewar sanarwar, 'yan tawayen sun kai hare-haren ne, yayin da tawagar MONUSCO da ke aikin tabbatar da kiyaye zaman lafiya ke marawa matakin da dakarun kasar Congo (FARDC) ke dauka na kare rayukan fararen hula da ke yankin Kiwanja-Rutshuru, kimanin kilomita 25 daga arewacin Goma, babban birnin jihar Arewacin Kivu.
Bugu da kari, a cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya aike da sakon ta'aziya da jaje ga iyalan wadanda hare-hare suka shafa da kuma gwamnatin kasar Tanzaniya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, MDD tana nan a kan bakarta na daukar dukkan matakan da suka wajaba bisa kudurorin kwamitin sulhu, don kare rayukan fararen hula da ke gabashin kasar ta jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC). (Ibrahim)