A ranar Talatan nan 22 ga wata, rundunar sojin Nigeriya ta tabbatar da kashe 'yan kungiyar Boko Haram akalla guda 37 a wani samame na hadin gwiwwa tare da sojin mayakan sama da suka kai wata maboyarsu, in ji kakakin rundunar sojin kasar kaftin Aliyu Danja.
Da yake bayyani ga manema labarai a garin Maiduguri, ya ce, rundunar ta hadin gwiwwa sun samu nasarar kai samamen ne a wata maboyar 'yan kungiyar dake Alagarno, a kudancin jihar Borno kuma nan take suka hallaka guda 37, sauran kuma suka tsere da raunin bindiga.
Ya ce, a lokacin wannan samame, sojojin sun samo makamai da albarusai masu yawa, sannan suka lalata motocin 'yan kungiyar guda uku da baburan hawa da dama a wannan maboyar.
Wannan samaman na sojojin dai ya zo ne kasa da awonni 48 da wadansu da ake zargin 'yan kungiyar ne suka hallaka mutane 20 a jihar ta Borno.
Talatan da ta gabata ne sojojin Nigeriyan suka sanar da kashe 'ya'yan kungiyar 40 a jihar ta Borno lokacin wata arangama da suka yi bayan an gano shirin da suke yi na tada bama-bamai a garuruwa 3 wato Bama, Gwoza da kuma Pulka. (Fatimah)