in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta dauki niyyar janye jikin jakadanta daga Aljeriya
2013-10-31 16:04:32 cri

Kasar Morocco ta janye jikin jakadanta dake kasar Aljeriya a ranar Laraba domin tattaunawa, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na MAP ya bayar dake ambato wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar Morocco.

Ma'aikatar harkokin wajen Morocco ta bayyana daukar wannan mataki bayan karuwar wasu ayyukan bata hali da na rikici daga kasar Aljeriya kan kasar Marocco, musammun ma game da takaddamar da ta shafi yankin Sahara.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar Marocco, babban dalilin hakan shi ne, wasikar da shugaban kasar Aljeriya ya aika a ranar 28 ga watan Oktoba a yayin wani taro a Abuja dake bayyana kiyayya kan kasar Morocco da kuma wani yunkurin shugaban Aljeriya na hana ruwa guda game da batun warware rikicin dake tsakanin kasashen biyu.

A tsawon lokacin da janye jikin jadakan zai dauka domin tattaunawa, hukumomin diplomasiyya da na kananan jakadun kasar Morocco dake kasar Aljeriya za su ci gaba da aiki a karkashin wani jami'an kula da harkoki na kasar, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China