in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya za ta tsaurara dokar yaki da ta'addanci
2013-10-08 09:41:22 cri

Gwamnatin kasar Algeriya na shirin tsaurara dokar da ta jibanci yaki da ta'addanci ta hanyar sake nazarin wadda ake da ita a yanzu, kamar yadda wata majiya ta kamfanin dillancin labaran kasar APS ta sanar a ranar Litinin din nan.

Majiyar ta yi bayanin cewa, sabuwar dokar da ake tsarawa yanzu wadda za'a mika wa majalissar dokokin kasar domin amincewa da ita na da nufin tafiya daidai da dokokin da kasa da kasa suka tsara da kuma Algeriyan ta rattaba wa hannu, musamman wadanda suka shafi matse hannu ga kudin tallafi ga kungiyoyin dake da alaka da 'yan ta'adda, hana tare da shawo kan ta'addancin.

Wannan dokar har ila yau tana bukatar a lissafa wassu dabi'u da ke da nasaba da ta'addanci wanda aka lissafa a cikin dabi'u na kasa da kasa kuma Algeriyan ta rattaba wa hannu, kamar wadanda ke da alaka da kafar samun kudade ga 'yan ta'adda, amfani da ko wace irin hanyar sufuri mai alaka da ta'addanci, kai hari da ababen fashewa da kuma kayayyakin nukiliya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China