A ranar Laraba 30 ga watan nan da muke ciki ne kasar Sin ta sake samun damar lashe kuri'un kasancewa memba, a majalissar tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta MDD, ko ECOSOC a takaice.
Kasar ta Sin ta samu wannan dama ce bayan lashe daukacin kuri'u 187, da mambobin MDDr suka kada, yayin babban zaman taron majalissar na 68 da ke gudanarwa a birnin New York na kasar Amurka. Za kuma ta ci gaba da kasancewa wakiliya a wannan majalissa tun bayan shigar ta a shekarar 1972.
An kafa majalissar ta ECOSOC ne dai tun a shekarar 1946, da zummar gudanar da tsare-tsaren ayyukan MDD, da ragowar hukumominta, wadanda suka jibanci tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ana kuma zabar mambobinta 54 ne, yayin babban taron majalissar, don gudanar da aiki na tsahon shekaru uku uku. (Saminu)