in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hari kan babbar hanya a arewacin Nigeriya ya janyo asarar rayukan mutane 10
2013-10-21 10:20:52 cri

A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeriya, akalla mutane 10 ne suka hallaka a wani hari da wassu mutane da aka zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai musu a kan hanyarsu ta zuwa Logumani, wani dan gari dake kusa da kan iyaka da kasar Kamaru.

Maharan da suke kan babura sun kai harin ne ga matafiyan da sanyin safiyar ranar Lahadin nan, in ji wani wanda ya gane ma idanunsa wannan lamari.

Ya zuwa lokacin da labarin ya zo mana, mahukunta na gwamnati ko 'yan kungiyar ta Boko Haram din ba su tabbatar da aukuwar hakan ba tukuna, ganin yadda a 'yan lokutan baya bayan nan kungiyar take shan matsin lamba daga rundunar tsaron a jihar ta Borno.

Sojoji a Nigeriya a ranar Talatan da ta gabata sun sanar da kashe akalla mutane 40 da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ne ta Boko Haram wadanda ake zargin suna da hannu a cikin yawan hare-haren da ake ta kaiwa fararen hula a garuruwan Bama, Gwoza da kuma Pulka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China