in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Mozambique sun kai samame a maboyar 'yan tawaye
2013-10-22 10:47:25 cri

Dakarun sojan kasar Mozambique sun kai samame a maboyar jagorar 'yan tawayen Renamo a cikin wata daji dake tsakiyar yankin Sofala, sai dai shugaban 'yan tawayen Afonso Dhlakama ya samu nasarar tserewa.

Rundunar tsaron kasar ta tabbatar a ranar Litinin din nan 21 ga wata cewa, sojojinta sun kai samame a yankin mai duwatsu na Satungira, inda suka zagaye shi har tsawon kwanaki biyu kafin su afka wa maboyar 'yan tawayen.

Wannan samame, in ji rundunar tsaron, ya tilasta wa shugaban 'yan tawayen Afonso Dhlakama tserewa daga gidan nashi, inda yake zaune fiye da shekara daya, kuma hakan ya sa kungiyar ta sanar da cewa, an dakatar da yarjejeniyar sulhu ta tsawon shekaru 21 da ta cimma da gwamnati, abin da yanzu haka ya kawo fargaban barkewar yaki.

Sakamakon wannan samame, kakakin kungiyar ta Renamo, Fernando Mazanga ya shaida wa manema labarai cewa, wannan samame da aka kai musu ya ba da alama ta dakatar da yarjejeniyar sulhu ta shekaru 21 da suka saka wa hannu tare da gwamnatin Mozambique.

A nashi bayanin, kanar Christopher Chume, babban darekta na tsare-tsare na rundunar tsaron kasar ya ce, abin damuwa akai yanzu shi ne yadda za'a dawo da zaman lafiya a yankin na Satungira, yana mai bayanin cewa, wannan samame na iya tunzura wani matakin na ramuwar gayya, amma ya tabbatar da cewa, babu yiwuwar fara yaki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China