An saki mutane hudu, 'yan kasar Faransa da suka yi aiki a kamfanin lantarki na Arewa na kasar Faransa wadanda kungiyar Al-Qaida, reshen yankin Maghreb wato AQMI ta sace su a cikin watan Satumban shekarar 2010 a garin Arlit dake arewacin kasar Nijar a ranar Talata, a cewar hukumomin Nijar.
Wadannan tsoffin mutanen da aka yi garkuwa da su wato Thierry Dol, Daniel Larribe, Pierre Legrand da Marc Feret, ga dukkan alamu suna cikin koshin lafiya bayan shugaban kasar Nijar Mamadou Issouffou ya tarbe su a ranar Talata da yamma a filin saukar jiragen soja dake birnin Niamey wanda kuma ya mika su ga hannun ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius da ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian da suka isa birnin Niamey.
A halin yanzu, suna ofishin jakadancin kasar Faransa dake Niamey kuma za su koma kasarsu ranar gobe, in ji shugaban kasar Nijar.
A cewar shugaba Mahamadou Issoufou, an sako su ne tare da taimakon shiga tsakanin wasu jami'an Nijar da kuma taimakon shugaban kasar Faransa, Francois Hollande. (Maman Ada)