in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai nazarci shirin yiwa sashen sarrafa fatu garan bawul
2013-10-23 10:30:49 cri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti mai mutane 17, wanda zai nazarci, tare da baiwa mahukuntan kasar shawarwari kan shirin yiwa sashen sarrafa fatu garan bawul.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da kwamitin, ministan ma'aikatar ciniki, masana'antu da harkokin zuba jari Mr. Olusegun Aganga, ya ce, an yanke shawarar kafa wannan kwamiti ne, domin ya baiwa gwamnatin managartan shawarwarin samar da ci gaba, a sashen sarrafa fatu, musamman ganin irin damar da kasar ke da ita, ta samun bunkasuwa a wannan fanni. Aganga ya ce, hakan zai baiwa Najeriyar damar fadada hanyoyinta na samun kudaden shiga, da samar da karin guraben ayyukan yi, ta yadda kasar ke iya zama ta daya a dukkanin fadin Afirka, ta kuma zama ta 10 a dukkanin fadin duniya a wannan fanni.

A jawabin da ya gabatar a madadin sauran mambobin kwamitin, mataimakin shugaban kwamitin, kuma shugaban kungiyar kamfanonin sarrafa fatu da dangoginta Alhaji Bashir Danyaro, cewa ya yi, kafuwar kwamitin ya zo a daidai lokacin da ya dace, za kuma su yi iyakacin kokari wajen gabatarwa gwamnati, irin shawarwarin da za su daukaka sashen sana'ar sarrafa fatu zuwa matsayi na gaba.

Kwamitin dai na da Alhaji Salisu Umar a matsayin shugaba, yayin da sauran mambobinsa suka hada da wakilan ma'aikatar kudi, da na ma'aikatar ayyukan gona, da hukumar bunkasa kananan masana'antu da dai sauransu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China