A ranar Laraba, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi maraba da matakan da aka dauka na yaki da matsalar tsaro a tekun tsakiya da yammacin Afrika, inda ya yi kira ga kasashe su aiwatar da matakan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun MDD ya bayar na mai bayyana cewa, magatakardan ya yi maraba da matakan kawarwa da kuma dakile harkokin masu fashin teku, 'yan fashi da makamai a jiragen ruwa da dai sauran laifuffuka da ake aikatawa a kan teku a yankin tsakiya da yammacin Afirka.
Sanarwar ta kara da cewa, matakan za su zamo shimfidar kafa dokoki kan wannan batu.
Ban, har wa yau, ya yabi kasashe da kungiyoyin yankin dangane da yadda suka yi shawarwari da juna da kuma yin kokari tare, don shawo kai da kuma kawar da fashin teku.
A halin da ake ciki, magatakardan na MDD ya bukaci masu ruwa da tsaki a yankin da su sa hannu su kuma aiwatar da matakan, tare da yin kira ga abokan hulda na kasa da kasa da su samar da muhimman ababan bukata.
Harkar fashin teku a Gulf na Guinea na cinyewa kasashen yankunan kudade da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 2 a kowace shekara ga kuma karin barazana da harkar ke kawowa yankin mai arzikin man fetur. (Lami)