in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya yi tir da kisan wani ma'aikacin wanzar da zaman lafiya a DRC
2013-08-29 15:20:47 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Laraban nan ya yi tir da kisan wani ma'aikacin wanzar da zaman lafiya, 'dan asaslin kasar Tanzaniya, sannan aka jikkata wassu guda 10 a lokacin wani sabon arangama a kudancin kasar jamhuriyar demokradiya na Congo DRC duk a rana daya.

A cikin bayanin da aka fitar ma manema labarai, wannan harin dai ya faru ne lokacin da hukumar wanzar da zaman lafiyar ta majalissar a kasar suka goyi bayan ayyukan sojojin kasar ta Congo don su kare lafiyar fararen hula dake zaune a garin Goma.

Mr. Ban ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma jajensa da wadanda suka raunana, da ma ita kanta gwamnatin kasar Tanzaniya.

Zaman dar dar a yankin yana karuwa bayan da kungiyar M23 suka bayyana a fili cewar, kungiyar wanzar da zaman lafiyar ta MDD MONUSCO ta hada baki da gwamnatin kasar, inda ta samar masu karin dakarun soja, abin da ya saba yarjejeniyar da aka cimma a birnin Kampala. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China