in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya ranar 25 da watan Oktoba a matsayin ranar babban zaben Madagascar
2013-08-23 11:59:04 cri

An sanar da ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a kada kuri'u a zagaye na farko, na babban zaben kasar Madagascar.

Shugaban hukumar gudanar da zaben kasar CENIT, Mr. Atallah Beatrice ne ya bayyana hakan ranar Alhamis 22 ga watan nan. Beatrice ya kara da cewa, idan har zagayen farko na zaben bai samar da cikakkiyar nasara ga daya daga 'yan takara 33 da za su fafata a zaben ba, za a gudanar da zagaye na biyu, tare da zaben 'yan majalissun dokoki a ranar 20 ga watan Disamba.

Tuni dai, a cewarsa hukumar ta CENIT, ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zabe, bisa shawarar kwararru daga MDD.

Idan dai za a iya tunawa wannan tsibiri na Madagascar, ya tsunduma cikin rikicin siyasa ne tun cikin shekarar 2008, inda kuma a farkon shekarar 2009, shugaba Rajoelina, ya daure karagar mulkin kasar, bayan hambarar da gwamnatin Marc Ravalomanana ta hanyar abin da kasashen duniya da dama ke kallo a matsayin juyin mulkin soji.

A halin da ake ciki dai, kungiyar nan ta bunkasa kasashen Kudancin Afirka ko SADC a takaice, na fatan gudanar da sahihin zabe a wannan tsibiri, zai kawo karshen takaddamar siyasa da ta ki ci ta ki cinyewa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China