Shugaban rikon kwarya na kasar Madagascar, Andry Rajoelina, ya yi kira ga kotun shirya zaben kasar ta musamman(CES) da ta jinkirta gudanar da zaben kasar da wata guda.
Mr. Rajoelina wanda shi ma ke takarar neman mukamin shugaban kasar, ya bayyana cikin wasikar da ya aikawa kotun shirya zaben kasar ta musamman cewa, idan har aka haramtawa dukkan 'yan takara daga cikin jami'an rikon kwaryar kasar 109 wadanda kungiyar AU ta haramtawa tsaya wa takarar mukamin tun a shekarar 2009 shiga zaben, to shi ma zai janye daga takarar.
Bisa doka, idan har shugaban rikon kwarya yana son tsayawa takara, kamata ya yi ya ajiye mukaminsa kwanaki 60 kafin ranar zabe, kana a nada shugaban majalisar dattawa domin ya shugabanci kasar.
Galibin jami'an da ke cikin gwamnatin rikon kwaryar kasar ba su son ajiye mukamansu saboda gudun cewa, ba za a gudanar da zaben kamar yadda aka shirya ba.(Ibrahim)