A ranar Alhamis 24 ga wata, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya yi alkawarin murkushe duk wata turjiya da kungiyoyi masu dauke da makamai suke yi, tare da ganin ya samu nasara a kan kungiyar 'yan adawa da gwamnatin nan wato Revolutionary Front zuwa nan da karshen shekarar da muke ciki.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar SUNA ya ruwaito, shugaba al-Bashir, a lokacin da yake bayani ga jama'a a wata gangami a jihar Arewacin Kordofan, ya ce, wannan shekarar za ta kawo karshen kungiyoyin adawa da kuma 'yan tawayen 'Revolutionary Front'.
Ya yi bayanin cewa, ana maraba da wadanda suke son zaman lafiya, amma wadanda ke neman akasin haka wato gurgunta manufofin gwamnati ta hanyar tada hankulan jama'a za su fuskanci bindiga, yana mai kiran 'yan tawayen da sunan 'yan zagon kasa.
Shugaba al-Bashir ya isa jihar Arewacin Kordofan din ne a safiyar Alhamis domin kaddamar da wassu ayyukan cigaba da aka yi a jihar da suka hada da samar da ruwan sha. Ita dai jihar Arewacin Kordofan tana makwabtaka da jihar Kudancin kordofan da suka dade suna arangama da dakarun SPLM, reshen arewacin kasar tun shekarar ta 2011.
A watan Afrilu, kungiyar Revolutionary Front wadda ta hada kan reshen SPLM na arewa da wassu manyan kungiyoyin adawa a Darfur guda uku sun kai hari a jihohin Arewaci da Kudancin kordofan.
Sun taba kwace wassu manyan wurare a Abu Karshula kafin gwamnati ta sake kwacewa bayan wata daya. (Fatimah)