Adadin mutanen da suka mutu a yayin zanga-zangar baya bayan nan a birnin Khartoum na kasar Sudan tun ranar 23 ga watan Satumban da ya gabata ya kai tsakanin 60 zuwa 70, in ji wani jami'in gwamnatin kasar.
An tabbatar da adadin ne bayan da ofishin ministan kiwon lafiya ya gudanar da rajistan mutanen da suka mutu da ba'a yi rajista ba a cikin asibitoci da dakunan ajiyar gawa, in ji Abdul-Rahman Al-Khader, gwamnan da'irar birnin Khartoum a yayin wata ganawarsa tare da shugabannin jam'iyyun siyasa na kasar a ranar Talata.
Mista Al-Khader ya bayyana cewa, ana cigaba da gudanar da wasu bincike domin gano mutanen dake da hannu kan wadannan tashe-tashen hankali, tare da nuna cewa, jami'an tsaro ba su da alhaki kan mutuwar masu zanga-zanga.
A ranar 23 ga watan Satumba, mutanen kasar Sudan sun gudanar da zanga-zanga a birnin Khartoum da wasu biranen kasar bayan da gwamnatin Sudan ta sanar da kara farashin kudin man fetur bisa tsarinta na tsuke bakin aljihu domin sake bunkasa tattalin arzikin kasar.
Wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa sun bayyana cewa, mutanen da suka mutu a yayin zanga-zanga a kasar Sudan ya haura 200, sai dai hukumomin Khartoum sun karyata wannan adadi. (Maman Ada)




