in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zanga-zanga ta sabbaba rasuwar mutane 29 a kasar Sudan
2013-09-27 09:33:05 cri

Rahotanni daga rundunar 'yan sandan kasar Sudan na cewa, kimanin mutane 29 ne suka rasu, ciki hadda jami'an rundunar sakamakon zanga-zangar nuna adawa da janye wani yanki na tallafin man fetir da gwamnatin kasar ke samarwa.

Wata sanarwa daga rundunar 'yan sandan wadda kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya samu kwafi, ta nuna cewa, baya ga wadanda suka rasu, tsakanin kwanaki 3 da fara zanga-zangar a Khartoum, babban birnin kasar, da kuma jihar Gezira, wasu karin mutane da dama sun samu raunuka.

Yanzu haka dai jami'an tsaro sun shiga farautar bata gari a sassan kasar ta Sudan, inda tuni aka cafke daruruwan mutane da ake zargin na da hannu wajen tada zaune tsaye. Har ila yau, an bayyana mai da da dama daga kayayyakin da wasu bata gari suka rika diba a matsayin ganima yayin tarzomar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai, mahukuntan kasar ta Sudan suka ayyana kara kudin man fetir, a shirin da ake yi na farfado da tattalin arzikin kasar, wanda ke cikin wani mawuyacin hali, tun bayan samun 'yancin kan yankin Sudan ta Kudu mai arzikin mai a shekarar 2011. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China