Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua dake jihar Ikko a tarayyar Najeriya ya samo mana labarin cewa, a ranar Litini 11 ga wata, aka saki matukan jirgin ruwa dake aiki da wani kamfanin kasar Birtaniya su uku da wadansu masu dauke da makamai suka sace.
A cikin wata sanarwa da kamfanin da wadannann mutane ke ma aiki 'Carisbrooke Shipping' ya bayar, wadanda suke aikin jigilar manyan kaya sun ce, matukan suna cikin koshin lafiya da kuzari bayan garkuwa da aka yi da su har na tsawon kwanaki 31.
Su dai mutanen uku wadansu masu dauke da makamai suka sace su a cikin jirgin nasu a daidai tazaran mil 80 daga gabar tekun kudancin kasar a ranar 7 ga watan Fabrairu.
A cewar sanarwar, masu dauke da makamai sun shiga cikin wannan jirgin ruwan mai jigilar manyan kaya tare da binciken shi gaba daya a kan ruwan kasa da kasa na gabar Guinea kafin su yi awon gaba da matukan shi.
Sai dai kamfanin bai sanar da ko ya ba da diyya kafin a sako masa matukan ba ko a'a.(Fatimah)