in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta samar da kayayyakin jiyya ga kasar Mozambique
2013-02-19 10:55:05 cri

A ranar Litinin 18 ga watan nan ne aka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar samar da kayan kula da lafiya, da kimar su ta kai dalar Amurka miliyan 1.6, tsakanin gwamnatin kasar Sin da kasar Mozambique.

Karkashin yarjejeniyar, kasar Sin za ta samar da tarin kayayyakin lura da lafiya na sashen hakora, wadanda za a yi amfani da su a babban asibitin kasar ta Mozambique.

Yayin da yake sanya hannu kan yarjejeniyar, jakadan kasar ta Sin a Mozambique Li Chunhua, ya ce, kasarsa na fatan ganin an samu ci gaba a fannin kiwon lafiyar al'umma. Shi ma a nasa bangare, ministan lafiyar kasar Mozambique Alexandre Manguele, bayyana godiyar kasarsa ya yi, don gane da wannan goma ta arziki, yana mai cewa, samar da wadannan kayan aiki, wata alama ce dake nuna kyakkyawar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. A cewarsa, yanzu haka ma akwai likitocin kasar ta Sin 17, dake aiki tare da takwarorinsu 'yan kasa domin habaka harkokin kiwon lafiya.

A shekarar da ta gabata ma dai, kasar ta Sin ta bai wa asibitin sojojin kasar dake Maputo kayayyakin aikin jiyya har karo 2, karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China