Rahotanni daga birnin Alkahira na kasar Masar na bayyana cewa, an maida tsohon shugaban kasar Husni Mubarak, zuwa wani asibitin sojoji dake Maadi, daga gidin yarin Tora da a baya yake tsare.
Wannan mataki, a cewar wani gidan talabijin mallakar kasar, ya biyo bayan umarnin sakin tsohon shugaban da wata babbar kotun kasar ta bayar, bayan ta wanke shi daga tuhumar aikata laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa.
Sai dai la'akari da halin dokar ta-bace da ake ciki, ya sa firaministan gwamnatin rikon kwaryar kasar Hazem Al-Beblawi, ya ba da umarnin yi wa Mubarak din dauri talala a gida, yayin da shi kuma tsohon shugaban ya zabi kasancewa a asibiti maimakon zama a gidansa, domin samun kulawar jami'an lafiya.
Baya ga daurin talala da a yanzu haka yake fuskanta, an kuma haramtawa Mubarak fita daga kasar, kasancewa har yanzu yana fuskantar karin zarge-zarge masu alaka da ba da umarnin kisan masu zanga-zanga a shekarar 2011. Za kuma a ci gaba da wannan shari'a a ranar Asabar mai zuwa. (Saminu)