Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya sake gurfana a gaban kotu a ranar Lahadi bisa zargin da ake masa na tunzura mutane zuwa tashe tashen hankali da kuma ba da umurnin kashe masu zanga zanga dake adawa da shi, in ji wani gidan talabijin din kasar. Mista Mubarak dai, ya samu sakin talala a ranar Laraba kan zargin cin hanci da rashawa. Haka kuma tsohon shugaban kasar da yaransa biyu ba su bayyana ba a gaban kotun karshe game da shari'ar da ake masu kan cin hanci da rashawa bisa dalilan tsaro ganin kasar, har yanzu tana fama da tashe tashen hankali bayan da hukumomin kasar suka tarwatsa magoya bayan Mohamed Morsi da karfin damtse.
Babban mataimakin rundunar sojojin kasar kuma faraminista Hazem Beblawi ya ba da umurni a ranar Alhamis na cigaba da tsare shi bisa dalilin dokar ta bacin wata guda dake aiki a cikin kasar tun daga ranar 14 ga watan Agusta. Mista Mubarak dai ya bukaci a cigaba da jinyarsa a cikin asibitin sojan Maadi kuma tsare shi ake a halin yanzu zai kare bayan da aka dage dokar ta baci a cikin kasar. (Maman Ada)